Bayanin mene ne Zakka
Ma'anar Zakka A
Larabci
Ita ce, Qaruwa da
havaka
Ma'anar Zakka A
Shari'a
Wani kaso ne na kuxi
da a ka iyakance, wanda ake fitar da shi a wani lokaci sananne, a ba wasu
mutane iyakantattu.
Matsayin Zakka
Zakka farillace daga
cikin farillan addinin musulunci, kuma ita ce rukuni na uku daga rukunan
musulunci. Allah ya ce, “Ku tsayar da salla ku ba da zakka” (Annur : 56).
Manzon Allah ( صلى
الله عليه وسلم ) ya ce, “An gina musulunci a
bisa abubuwa biyar, shaidawa babu abin bautawa bisa cancanta sai Allah, kuma
Muhammad bawansa ne Manzonsa ne. Da tsaida sallah, da ba da zakka, da ziyartar
xakin Allah, da azumin watan Ramadan” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi]
Hukuncin Wanda Ya Hana
Zakka
Wanda ya hana zakka
zai iya zama ya hana ne don bai yarda da ita ba, ko kuma saboda rowa.
1 - Wanda Ya Hana
Zakka Saboda Bai Yarda Da Ita Ba
Duk wanda ya musunta
wajabcin zakka alhali ya san wajibi ce, to ya zama kafiri, da ijma’in malamai,
saboda ya qaryata Allah da Manzonsa.
Sayyidina Abubakar ya
yaqi wanxanda suka qi ba da zakka, ya ce, “Wallahi sai na yaqi wanda ya raba tsakanin sallah da zakka
(wato ya yarda zai yi sallah, amma ya ce, ba zai ba da zakka ba) saboda zakka
haqqin dukiya ne, ya ce, wallahi da za su hana ni dabaibayi wanda suke bawa
Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) da na yaqe su a kansa” [Bukhari ne ya rawaito shi].
2 - Wanda Ya Hana
Zakka Saboda Rowa
Wanda ya hana zakka
saboda rowa, za a yi mata tilas a karva, amma bai zama kafiri ba, sai dai ya yi
laifi babba, ya yi zunubi mai girma.
Saboda faxin Manzon
Allah ( صلى الله عليه وسلم ) kan wanda ya hana zakka, ya ce, “Babu wani ma’abocin zinare ko azurfa wanda ba
ya bayar da haqqisu face sai ya kasance ranar alqiyama an mayar da su alluna na
wuta, a gasa su a wutar Jahannama, sannan akan goshinsa da bayansa da gefensa
da su, duk lokacin da suka yi sanyi sai a sake gasa masa su, a cikin wani yini
tsawonsa shekara dubu hamsin, har sai an yi hukunci tsakanin bayi, sai ya ga
hanyarsa, ko dai zuwa Aljannah, ko kuma zuwa Wuta” [Muslim ne ya rawaito shi]
Idan ya fito yaqi don
hana zakka, to sai a yaqe shi, har ya ya miqa wuya ga umarnin Allah mai girma
da buwaya, ya bayar da zakka. Saboda faxin Allah Maxaukakin Sarki “Idan sun tuba sun tsayar da sallah, sun ba da zakka to ku qyale
su”. (Attauba : 5).
Da faxin Manzon Allah
( صلى الله عليه وسلم ) “An umarceni in yaqi
mutane, har sai sun shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma
Muhammad Manzon Allah, su tsaida sallah, su bayar da zakka. Idan sun yi haka
jininsu ya tsaru gare ni da dukiyoyinsu, sai da haqqin musulunci, hisabinsu
kuma yana wurin Allah” [Bukhari da Muslim ne
suka rawaito shi].
Hikimar Wajabta Zakka
1 – Tsarkake zukata da
wanke su daga rowa, da zunubai. Allah mai girma da buwaya ya ce, “Ka karvi zakka daga cikin dukiyarsu, ka tsarkake su ka wanke su
da ita” (Attauba : 103).
2 – Tsarkake dukiya da
havaka ta, da saukar albarka a cikinta, saboda faxin Annabi ( صلى الله عليه
وسلم ) “Sadaka ba ta rage
dukiya”[Muslim ne ya rawaito
shi]
3 – Jarraba bawa cikin
bin umarnin Allah, da gabatar da son Allah akan son dukiya.
4 – Taimakawa talakawa
da biya musu buqata, abin da yake qara soyayya, kuma ya tabbatar da kyakkyawar
zamantakewa tsakanin xaixaikun musulmi.
5 – Sabawa da bayarwa
da ciyarwa a kan tafarkin Allah.
Falalar Zakka
1 – Sanadi ne na samun
rahamar Allah. Allah mai girma da buwaya ya ce, “Rahamata ta
yalwaci komai da komai, zan rubuta ta ga waxanda suke kiyaye dokokina suke ba
da zakka” (Al-a'araf : 156).
2 – Sharaxi ne na
samun taimakon Allah. Allah ya ce, “Allah yana
taimakon wanda ya taimake shi, haqiqa Allah mai qarfi ne mabuwayi. Waxanda idan
muka tabbatar da su a bayan qasa sai su tsaida sallah su bayar da zakka”(Al-hajj : 40 – 41).
3 – Sanadi ne na
kankare zunubai. Annabi (r) ya ce, “Sadaka tana kankare zunubai kamar yadda ruwa yake kashe wuta”[Tirmizi ne ya rawaito shi]
Dukiyar Da Zakka Da
Wajaba A Cikinsu
Sharuxxan Wajabcin
Zakka
1 – Musulunci
Zakkar kafiri ba ta
inganta ba, saboda Allah Maxaukakin Sarki ba ya karvar aikin kafirai
2 – ‘Yanci.
Ba ta wajaba a kan
bawa, saboda dukiyarsa mallakar Ubangidansa ce.
3 – Mallakar Nisabi
Bayanin Nisabi
Nisabi shi ne:
Wani kaso ne na kuxi,
wanda idan kuxi suka kai shi zakka ta wajaba a cikinsu
Sharuxxan Nisabi
A – Nisabin ya zama ya
qaru a kan buqatar mai dukiyar, wadda ba zai iya wadatuwa daga barinta ba,
kamar ci, tufafi, wurin zama, saboda zakka ta wajaba ne saboda tausayawa
talakawa, don haka wajibi ne shi ma mai dukiyar ya zama ba ya buqata.
B – Nisabin ya zama
mallakar mutum ne, mallaka cikakkiya, zakka ba ta wajaba a cikin dukiyar da ba
mallakar wani mutum ba ce, kamar dukiyar da aka tara don gina masallaci, ko
dukiyar da aka waqafinta don amfanin kowa da kowa, ko dukiyar qungiyoyin jin
qai da ayyukan alheri.
4 – Zagayowar Shekara
A kan Dukiyar
Shekara ana nufin:
Shekarar musulunci
cikakkayi ta hijira.
Nisabi ya zama ya yi
shekara guda a wurin wanda ya mallake shi, wata goma sha biyu. Sai dai wannan
sharaxi na kewayowar shekara guda a kan nisabi ya taqaita ne a kan kuxi, da
kayan kasuwanci, da dabbobin ni’ima.
Amma kayan gona da na
marmari da ma’adinai da dukiyar da aka samu a qasa ba sharaxi ne sai shakara ta
kewayo ba